Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda da haɗin gwiwa na kwamitin koda ta kwana da gwamnatin Katsina ta kafa sun sami nasarar kama mutane tara da ake zargi da karkatar da abincin gina jiki na ƙananan yara da ke fama da cutar tamuwa a Katsina.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fatar da sanarwar haka,mace ce, Amina Abdulrahaman aka fara kamawa yar shekara 46 da ke zaune a Mobil Quarters cikin garin Katsina ɗauke da ‘yan ƙwamaso guda 600.
Wanda ake zargi ta tabbatar da cewa ta saya a hannun wani mutum da a halin yanzu ake nema ruwa a jallo.
DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa a kasuwar Mashi na ƙaramar hukumar Mashi da unguwar Kwaɗo a garin Katsina jami’an su sun kama mutane takwas da ake zargi da aikata irin wannan laifi.
Sun haɗa da A’isha Rabiu da Jamila Yahaya sai Farida Kabir da Shafa’atu Abubakar.
Suran sun haɗa da Maryam Kabir da Buhari usman waɗanda yanzu haka suna hannun hukuma.
DSP Abubakar Sadiq ya sanar da kama 1,624 ‘yan ƙwamaso a samame da jami’an tsaron suka kai a waɗannan wurare uku.
Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar CP Ali Umar Fage ya umarci jami’an sa su gudanar da cikakken bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a wajen karkatar da wannan abincin yara.
