Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan takarar gwamnan Kaduna na Jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Isa Mohammed Ashiru, ya zargi gwamnatin Kaduna da amfani da jami’an tsaro da ’yan daba wajen tarwatsa masu goyon bayan jam’iyyar da suka gudanar da tattakin haɗin kai a Kaduna.
Ashiru ya yi wannan zargin ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, bayan dubban magoya bayan ADC da wasu ’yan jihar suka taru a dandalin Murtala Sƙuare domin gudanar da tattaki.
Ya ce mahalarta tattakin sun fito ne cikin lumana domin bayyana goyon bayansu ga ADC da kuma buƙatar sauyi a jihar.
A cewarsa, jami’an tsaro da wasu ’yan daba da ya danganta da gwamnatin jam’iyyar APC ne suka tarwatsa taron tare da amfani da borkonon tsohuwa.
“Sun tsoratar da mutane, sun tursasa musu, sannan suka tarwatsa tattakin cikin lumana. Sun harba borkonon tsohuwa kan mutanen da ba su ɗauke da makami ba,” inji shi.
Mr Ashiru ya ce matakin na jami’an tsaro ba aikin tabbatar da doka ba ne, sai dai abin da ya bayyana a matsayin “tsananin fargabar siyasa” daga gwamnatin da ta kasa cika alkawuranta.
Ya ce ’yan jihar Kaduna ba za su daina amfani da hakkokinsu na tsarin mulki ba saboda barazana ko amfani da jami’an tsaro.
Ashiru ya zargi gwamnatin APC da cewa ba wannan ne karo na farko da take amfani da ƙarfi wajen dakile tarukan siyasa ba.
Ya yi iƙirarin cewa a baya an taɓa tarwatsa taruka, lalata kadarori tare da raunata wasu ’yan ƙasa.
Ashiru ya ce matsalolin da al’ummar Kaduna ke fuskanta, ciki har da tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin biyan albashi da kuma abin da ya kira “cika alkawura da aka karya”, ba za su sa mutane su koma yin shiru ba.
Ya ce magoya bayan ADC za su ci gaba da taruwa, bayyana ra’ayoyinsu da gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.
ɗan takarar ya ce tafiyar siyasar 2027 ba ta buƙatar izinin APC domin farawa, kuma ba za ta tsaya ba saboda abin da ya ce ya faru a Murtala Sƙuare.
