Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan shahararren mai sharhin siyasa, Ibrahim Khalil Danshagamu, wanda aka kai wa hari da makamai masu kaifi a gidansa da ke Unguwar Gaida, a ƙaramar Hukumar Kumbotso ta jihar.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, bayan Rundunar ’Yan Sandan ta samu kiran gaggawa daga Kwamandan ƙungiyar ’Yan Sa-kai ta Gaida, inda ya sanar da cewa wasu ’yan daba da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan marigayin da ƙarfi tare da kai masa hari.
Rundunar ta bayyana kamen ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ranar Laraba.
A cewar sanarwar, jami’an Rundunar ’Yan Sandan da ke Sashen Kumbotso sun gaggauta isa wurin da lamarin ya faru, inda suka ɗauki Danshagamu zuwa Asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed da ke Kano domin ceto rayuwarsa. Sai dai, likita ya tabbatar da cewa ya rasu ne bayan isarsa asibitin.
Kisan Danshagamu ya jawo kakkausar suka daga ’yan siyasa na adawa da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama, wadanda suka yi kira da a gudanar da cikakken bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya haddasa mutuwarsa da kuma gano waɗanda ke da hannu a kisan.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jigo a siyasar adawa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce an tsinci gawar Danshagamu cikin jini a gidansa.
Kwankwaso ya bayyana kisan a matsayin “mummunan hari” tare da kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta kafa kwamitin bincike na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata laifin.
Haka kuma, Amnesty International Nigeria ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai kira da a gudanar da cikakken bincike, musamman ganin cewa a tsarin dimokuraɗiyya ya kamata a kare masu bayyana ra’ayinsu da masu sukar gwamnati ko wasu hukumomi.
A nasa ɓangaren, Shugaban Jam’iyyar NDC na Jihar Kano, Husaini Mai Riga, ya bayyana kisan a matsayin abin “damuwa matuƙa kuma wanda ba za a amincewa da shi ba”, yana mai cewa lamarin na barazana ga ’yancin aikin jarida, tsaron al’umma da kuma kimar dimokuraɗiyya a jihar.
Rundunar ’Yan Sandan ta ce kamen mutanen biyun ya biyo bayan wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri, ƙarƙashin jagorancin Jami’in ’Yan Sandan Sashen Kumbotso, tare da hadin gwiwar sassan dabara na rundunar da kuma masu ruwa da tsaki a cikin al’umma. A cewar sanarwar, wadanda ake zargin suna tsare a hannun ’yan sanda, inda ake ci gaba da yi musu tambayoyi.
Rundunar ta kuma ce tana kara ƙaimi wajen zaƙulo tare da cafke duk wani mutum da ake zargin yana da hannu a kisan. Haka kuma, jami’an tsaro na ci gaba da karɓar bayanai daga mutanen da lamarin ya shafa, yayin da ake gudanar da binciken ƙwararru domin gano yadda harin ya faru da kuma dalilin da ya kai ga aikata shi.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya nuna damuwarsa kan lamarin tare da jajanta wa iyalan marigayin, yana mai tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an gano gaskiyar lamarin tare da tabbatar da an yi wa kowa adalci.
Ya ce, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano za ta ci gaba da sauke nauyin da aka dora mata na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar wa jama’ar jihar cewa za ta bi lamarin har zuwa matakin da ya dace.
Rundunar ta kuma yaba wa ƙungiyar ’Yan Sa-kai ta Gaida bisa gaggauta sanar da ’yan sanda bayan faruwar lamarin, tana mai cewa hakan ya nuna muhimmancin haɗin gwiwar al’umma da jami’an tsaro wajen dakile aikata laifuka.
Ta buƙaci mazauna yankin da su kara taka-tsan-tsan tare da sanar da jami’an tsaro duk wani sahihin bayani da zai taimaka wajen gano masu hannu a lamarin, ta hanyar zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma kiran layukan gaggawa na rundunar. Kiyawa ya ce, bincike kan lamarin yana ci gaba, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
A halin yanzu, rundunar ta ƙara yawan sintiri da ayyukan tattara bayanan sirri a Gaida da yankunan da ke makwabtaka da wurin, domin tabbatar da zaman lafiya da doka da oda tare da hana ɓarkewar wani rikici.
