Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta bayyana cewa, wata ƙaramar gobara ta tashi a tashar jirgin ƙasa ta Idu da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, sakamakon matsalar wutar lantarki.
Lamarin ya faru ne a ɗakin tsarin samar da lantarki mai ƙaramin ƙarfi (low-Voltage electrical room) na tashar a yammacin Laraba, inda aka gano gobarar da misalin ƙarfe 8:30 na dare. Hukumar ta ce, ma’aikatan kula da tashar sun yi gaggawar shawo kan gobarar, inda suka kashe ta cikin ɗan lokaci.
A cikin sanarwar da Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NRC, Callistus Unyimadu, ya fitar, hukumar ta ce binciken farko ya nuna cewa wasu igiyoyin samar da wutar lantarki da ke haɗe da na’urorin sarrafa tashar sun lalace.
Sai dai hukumar ta ce tsarin samar da wutar lantarki ta hasken rana da ake amfani da shi a matsayin madadin wutar lantarki bai samu matsala ba.
NRC ta ƙara da cewa an kuma dawo da wutar lantarki ga lif da kuma escalators na tashar na ɗan lokaci, inda daga cikin lif da escalators 29, guda 28 ke aiki a halin yanzu.
Hukumar ta tabbatar wa fasinjoji cewa gobarar ba ta shafi ayyukan jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna ba, inda ta ce za a ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen ƙasa kamar yadda aka tsara.
NRC ta ce tawagar ƙwararrun ma’aikatanta na gudanar da ƙarin bincike domin gano ainihin musabbabin matsalar tare da tabbatar da an gyara na’urorin da abin ya shafa gaba ɗaya.
Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja (AEDC) ma an sanar da ita game da lamarin domin ta bayar da tallafin fasaha da kuma ɗaukar matakan da suka dace.
