2027: Magoya bayan APC sun yi cincirindo a titinan Kaduna yayin da jam’iyyar ta ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Titina a birnin Kaduna sun cika da mutane da dama masu goyon bayan APC, yayin da jam’iyyar ta ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta gabanin zaɓukan 2027, inda aka samu wasu na rera “Tinubu, Uba Sani Twice”.

An tara jama’ar ne a yankunan manyan titina, ciki har da Yakubu Gowon Way, Independence Way, Waff Road da Golf Course Road, inda aka ga magoya baya ɗauke da tutocin APC, hotuna da wasu kayayyakin zaɓe suna rera waƙoƙin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani.

Dandazon ya haɗa mambobi, ƙungiyoyin matasa, mata da wasu masu goyon baya, waɗanda suka taru don nuna goyon bayansu ga jam’iyyar da kuma ‘yan takararta gabanin zaɓukan da ke tafe.

Wasu da suka zanta da manema labarai, sun bayyana gamsuwarsu ga ayyukan Tinubu da Uba Sani, inda suka ce aikace-aikacensu a matsayinsu sun ƙarfafa musu ƙwarin-gwiwar da suke da ita kan jam’iyyar. Wani daga cikinsu mai suna Haruna Isa, ya ce ya gamsu da alƙiblar gwamnatocin APC, inda ya ƙara da cewa jam’iyyar ta cancanci cigaba da samun goyon bayan ‘yan Nijeriya wajen warware matsalolin da suke addabar ƙasar.

Haka ma wani mai suna, John Solomon, wanda ya ce Uba Sani yi ayyukan da suka taimaka wajen inganta ababen more rayuwa da ci-gaba a Jihar Kaduna, yana mai cewa hakan ne zai ba shi nasara yayin zaɓukan. Kazalika, wata Aisha Umar ta bayyana cewa ta gamsu da ayyukan Tinubu da Uba Sani, musamman wajen inganta zamantakewar al’ummar Nijeriya da mazauna Jihar Kaduna.

By Babaji

Leave a Reply