2027: Shettima ya miƙa wa APC fom ɗin takarar Tinubu na zaɓen shugaban ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya miƙa fom ɗin nuna sha’awa da na tsaya wa takarar Shugaba Bola Tinubu ga jagororin ƙasa na jam’iyyar APC.

Shettima, wanda ya miƙa fom ɗin a Cibiyar Taro ta Ƙasa-da’Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, ya yi kira ga gwamnonin APC da ‘yan Majalisar Tarayya da su mara wa takarar Shugaban Ƙasar baya.

Ya ce, gwamnatin Tinubu ta fara kawo sauye-sauye masu anfani ta hanyar ajandar “Renewed Hope”, duk da ƙalubalen tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta.

Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, sun bayyana goyon bayansu ga takarar Tinubu, tare da yaba wa sauye-sauyen gwamnatinsa don amfanin al’ummar Nijeriya.

Haka kuma gwamnonin APC ƙarƙashin jagorancin Hope Uzodinma sun nuna cikakken goyon baya ga shugaban ƙasar gabanin zaɓen 2027 da ake cigaba da tunkara.

By Babaji