Ƴar aiki ta yi iƙirarin ita ta kashe ƴar alƙali, inji majiyar ƴan sandan Legas

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata ɗaya daga cikin ƴan aikin Aribemchukwu, wacce aka yanka ta har lahira, ta yi iƙirarin ta na hannu waje kisan uwar gidanta, kamar yadda ƴan sanda su ka bayyana a ranar Alhamis.

Aribemchukwu, wacce ƴa ce ga Alƙali Rita Ofili-Ajumogobia, an kashe ta ne a gidanta da ke Rukunin gidajen Parkview a yankin Ikoyi na Jihar Legas.

Wata majiya ta ce an kashe ta ne a ranar Talata yayin da aka tsinci gawarta a ƙofar gidanta a safiyar ranar Laraba.

An kama mutane uku da ke mata aiki da su ka haɗa da; mai aikin gida, mai gadi da kuma direba waɗanda a ke zargin su da hannu a kisan marigayiyar.

Wasu ƴan sanda da su ka buƙaci a ɓoye sunansu, sun ce yayin gudanar da binciken, ƴar aikin ta furta cewa ta na hannu a cikin kisan.

Sun kuma ce an kashe ta ne a wajen ɗakinta inda daga nan ne aka janyo ta zuwa wajen gidan nata.

Haka nan, sun ce waɗanda su ka yi kisan sun yi ta ƙoƙarin goge jini da ya zuba domin kar a kama su, amma sun bar wasu alamu saboda da dare su ka yi ɗanyen aikin inda bayan haka ne su ka kwashe ababenta masu daraja.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin ya ce su na cigaba da gudanar da bincike.

By Babaji