Ghana: Ministocin Tsaro da Muhalli sun rasu a hatsarin helikwafta

Spread the love

Ministan tsaron Ghana Dr Omane Boamah da na muhalli, Murtala Mohammed tare da wasu mutum shida sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a yau Laraba.

Lamarin ya rutsa da ma’aikatan jirgin uku a hatsarin jirgin mai saukar ungulu wanda ya faru a yankin Ashanti.

Shugaban ma’aikatan ƙasar Ghana Julius Debrah wanda ya yi jawabi ga al’ummar ƙasar ya umarci da a sassauto da tutoci domin nuna alhini.

Tun da farko wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar da safiyar yau, ta nuna cewa an daina jin ɗuriyar jirgin – mai saukar ungulu – bayan katsewar sadarwarsa.

Rahotonni sun ce mutanen da ke cikin jirgin sojin – mai lamba Z9 – na kan hanyarsu ta zuwa garin Obuasi mai arzikin ma’adinai domin halartar wani taro na ƙasa lokacin da hatsarin ya auku, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

By Babaji