
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malaman Makaratun Polytechnics ASUP, ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu na ta biya buƙatun da aka nemi ta sauke da ya shafi walwalar ma’aikata.
Shugaban ASUP. Shammah Kpanja a yayin wani zama na gaggawa ranar Alhamis a Abuja, ya bayyana mawuyacin halin da lakcarorin poly suke fuskanta duk da cewa gwamnatin ta yi alƙawarin warware matsalolin ƙungiyar da ta gabatar mata.
Ya ce, har yanzu hukumar albashi da kuɗaɗen shiga (NSIWC) ba ta a bayyana lokacin da za a fara biyan lakcarorin alawus ɗinsu na karantarwa ba, wanda a cewarsa yana daga cikin yarjejeniyar ASUP/FGN 2010.
Ya ƙara da cewa, a madadin samar da mafita game da lamarin biyan, an cire batun daga cikin kasafi, sannan Ma’aikatar Ilimi ta ƙi tsoma baki domin samar da mafita a kai.
Haka kuma, akwai bashin da suke bi na shekara guda, waɗanda an sanya shi a cikin kasafi, amma kuma har yanzu ba a fara biya ba bisa wasu dalilai da ƙungiyar ba ta gane musu ba.
Kazalika, Kpanja ya ce har yanzu wasu makaratun da ke ƙarƙashin gwamnatocin jihohi suna fuskantar matsalolin rashin fara biya da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na N70,000.
