
A yau Laraba Shugaba Bola Tinubu ya sanar da ayyana dokar ta-ɓaci akan harkokin tsaro a faɗin kasar, inda ya umarci rundunonin ƴan sanda da sojoji da su ƙara daukar ma’aikata domin ƙarfafa yaƙi da taɓarɓarewar matsalar tsaro a Nijeriya.
A wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya umarci ‘yan sanda da su ɗauki karin jami’ai 20,000 aiki, wanda hakan zai kai adadin waɗanda ake shirin ɗauka zuwa 50,000.
Haka kuma ya amince da amfani da sansanonin NYSC a matsayin wucin-gadi wajen horas da sababbin jami’an.
Sanarwar ta ce, “A yau, ganin halin tsaro da ake ciki, na yanke shawarar ayyana dokar ta-baci kan tsaro a faɗin ƙasa tare da bayar da umarnin karin daukar ma’aikata cikin rundunonin tsaro.
“Daga wannan sanarwa, an bai wa ‘yan sanda da sojoji izinin kara ɗaukar jami’ai. ‘Yan sanda za su kara daukar jami’ai 20,000, wanda zai kai adadin zuwa 50,000.
“Kodayake tun da farko na amince da inganta cibiyoyin horar da ‘yan sanda a fadin kasa, daga wannan sanarwa, hukumomin ‘yan sanda na da izinin amfani da sansanonin National Youth Service Corps a matsayin wuraren horo.
“Jami’an da za a cire daga tsare-tsaren VIP za a tura su horo na gaggawa domin sake horas da su tare da bunkasa ingancin ayyukan tsaro da za su bayar idan an tura su yankunan da ke fama da matsalar tsaro a ƙasar”, kamar yadda sanarwar da ƙara da cewa.
