Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haka kuma za a Ƙirƙiri irin wannan ƙananan cibiyoyi a ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina.
Cibiya ita ce ta biyu irinta a Najeriya kuma ta farko a matakin jiha da aka kafa domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a ƙasa da waje.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da cibiyar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan nasara a matsayin mataki nagari da ya daidaita a Katsina da ƙa’idojin kasuwanci na duniya, tare da buɗe sabbin damar bunƙasar tattalin arziƙi da faɗaɗa kasuwanni.
Ya ce ƙirƙiro cibiyar ya nuna himmar gwamnati wajen samar da yanayi mai kyau da ya dace da fara kasuwanci, bunƙasa shi, haɗin gwiwa, da kuma gogayya ba kawai a Najeriya ba har ma a ƙasashen duniya.
Gwamnan ya ƙara da cewa cibiyar za ta zama ginshiƙi wajen gudanar da shigo da kaya da fitar da su, wanda zai ƙara haɓaka gasa da inganta matsayin Katsina a kasuwannin duniya.
Ya ce lokacin da yake riƙe da mukamin darakta janaral na SMEDAN, Gwamna Raɗɗa ya ce ya kasance cikin tawagar da ta samar da Cibiyar Sauƙaƙe Kasuwanci ta ƙasa. “Yau gashi a Katsina na gina kan wannan tubali inda karo na farko a Arewa maso Yamma ake kawo tsarin kasuwanci na duniya a matakin jiha,”Inji Dikko Raɗɗa.
Gwamnan ya yi godiya ga masu ba da shawara, ma’aikatar kasuwanci da masana’antu, da dukkan abokan haɗin gwiwa da suka ba da gudunmawa wajen nasarar cibiyar.
Ya bayyana cewa ya riga ya ba da umarni na kafa ofisoshin sauƙaƙe kasuwanci a dukkan ƙananan hukumomi 34, domin sauƙaƙe harkokin kasuwanci, farfaɗo da tattalin arziƙin yankuna, da inganta rayuwar jama’a.
Ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma, bunƙasa tattalin arziƙi, tare da bai wa ‘yan kasuwa damar shiga kasuwannin duniya.
Tun da farko, Kwamishinan Kasuwanci da yawon shaƙatawa, Hon. Yusuf Jirdede, ya bayyana sabuwar cibiyar a matsayin ɗaya daga cikin manyan gadojin wannan gwamnati.
Ya ce shekarun da suka wuce kayayyakin Katsina sun tsaya a kasuwannin cikin gida kawai, amma wannan cibiya ta kawar da giɓin.”
