Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Farfesa sallau wanda Malami a jami’ar FUDMA da ke Dutsinma yana riƙe da sarautar Sarkin Askan Yarima Katsina Hakimin Safana .
Ya kuma taɓa riƙe muƙamin darakta a hukumar raya al’adu na jihar Katsina kafin ya koma jami’ar FUDMA.
A kwanakin baya ya taɓa faɗawa manema labarai cewa a matsayin sa na Farfesa bai hana shi sana’ar wanzaci ba.
Ni nakewa ɗalibai da malaman jami’ar aski su biyani,”Inji Farfesa.
Haka ma ya ce idan iyalan malaman jami’ar suka sami ƙaruwa “ni nake yi wa jaririn aski in cire belu a biya ni”Inji sallau
Sarkin askan ya bayyana cewa tun yana karatun firamare ya fara sana’ar wanzanici har yanzu da na zaman Farfesa ban bar sana’ar ba domin yana taimaka mani wajan ciyar da iyali na.
Ya bayyana cewa sana’ar wanzanici gado yayi daga mahaifinsa don haka ba zai bari ba a halin yanzu.
Sarkin Maganin ƙasar Hausa Alhaji Abdulrazaq Ture ya tabbatar masa da sarautar wanda naɗin ya gudana a ɗakin taro na ma’aikatar ilimi ta ƙasa dake birnin tarayyar Abuja.
Haka zalika, yan uwa da abokan arziki sun halacci naɗin tare da fatan alheri baki ɗaya.
Farfesa Bashir Aliyu sallau shine shugaban sashen koyar da Hausa a jami’ar FUDMA da ke Dutsinma a jihar Katsina.
