Matashi ya kammala digirinsa bayan shekara 10

Spread the love

Daga WAKILINMU

Wani bawan Allah mai suna Abba Abubakar Santalee ya bayyana farin cikinsa yayin da ya kammala karatun digirin farko a jami’ar ABU Zaria.

Abba Abubakar Santalee ya fito ya bayyana wannan abin alheri ne a shafinsa na Tuwita a ranar Talata.

Inda farin cikin Pharm. Abba Abubakar Santalee ya ke shi ne, ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin samun takardar shaidar Digiri a wannan babbar jami’a.

Da ya ke bayanin abin da ya sa ya daɗe bai gama karatun ba, Abba Abubakar Santalee ya ce, yajin-aikin aungiyar ASUU ya vata masa aƙalla shekara ɗaya.

Haka zalika, Abba Santalee ya gamu da qalubale a jami’ar ta Ahmadu Bello da ke gari Zaria, har ta kai ya ƙara shekaru uku kafin ya ci duka jarrabawansa.

A tsawon shekara goma da ya yi yana karatu ne kuma Ubangiji ya jarabci Abba Santalee da annobar Korona wanda ta jawo aka rufe duk makarantu.

Tun shekarar 2012 Santalee da sauran abokan karantunsa suka samu shiga jami’ar. Amma bai yi sallama da makarantar ba sai a watan Afrilun shekarar nan. 

By Editor