Wani ɗan Nijeriya mai suna Kunle Adeyanju wanda ya ke tattaki daga Landan zuwa Lagas, ya isa nahiyar Afrika.
Mutumin wanda yana tafiyar ne a kan babur ɗinsa ya sanar da hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Tuwita a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu.
Da ya ke sanar da isowarsa nahiyar Afrika, jarumin mazan ya wallafa wani hotonsa kusa da wata alama da ke nuna cewa lallai yana kusa da birnin Casablabca na ƙasar Moroko. Moroko na arewacin Afrika.
Wannan ce rana ta shida da fara tafiyar tasa, kasancewar ya fara ta ne a ranar 19 ga watan Afrilu, 2022.
Da wannan nisa da ya yi a tafiyar tasa, ba a sani ba ko tafiyar za ta ɗauke shi ƙasa da kwanaki 25 da ya shirya yi tun farko.
Kunle na tattakin ne domin tara kuɗi da zai tallafawa yaqi da cutar shan inna sannan ya taimaka wajen samar da tsafta. Yana ƙoƙarin tara naira miliyan 20.
