Wani matashin sauryai ɗan kimanin shekara 18, Chibuike Emmanuel, ya rasa rayuwarsa sanadin wutar lantarki a yankin Ozoro, ƙaramar hukumar Isoko North, jihar Delta.
Rahotanni sun bayyana cewa, wutar ta lantarke matashin ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Talata yayin da ya ke cajin wayarsa ƙirar iPhone 8 a tushen wayar lantarkin.
A cewar wata majiya ranar Laraba, ƙawar mahaifiyar matashin yaron ta kai rahoton abin da ya afku ofishin ‘yan sanda, wacce ta ɗauko mamacin daga jihar Legas domin ya yi hutunsa a tare da su.
Rahoto ya nuna cewa, matashin ya kwanta a kan siminti a gidan ƙawar mamansa da ke kan hanyar Idheze kuma ya ɗora iPhone ɗinsa a kan ƙirjinsa bayan ya jona cajin, sannan ya yi barci.
Majiyar ta ce, “yayin da ya ke cikin wannan yanayin ne wutar ta lantarke shi har lahira. An yi gaggawar kai shi asibitin Okeleke amma likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa.”
“Yanzu haka an kai gawar matashin yaron ɗakin aje gawarwaki mai zaman kansa da ke yankin Ozoro.”
Yayin da aka tuntuɓe shi, Kakakin rundunar an sanda reshen jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa.