Yadda ’yan sanda suka kai mana hari ba gaira, ba dalili – ’Yan Shi’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Harkar Musulunci a Nijeirya, waɗanda aka fi sani da ’yan shi’a, sun koka kan harin da jami’an ’yan sandan Nijeriya suka kai masu a yayin zanga-zangar nuna boyon baya ga al’ummar Falastinawa a Jihar Kaduna da garin Zariya.

A wani taron manema labarai da harkar ta gudanar a Jihar Kaduna ranar Litinin, wanda Yanusa Lawal Musa ya gabatar da madanin harkar, ya bayyana cewa, a duk ranar Juma’ar ƙarshe ta azumin watan Ramadan ana gudunar da zanga-zangar Qudus a duk faɗin duniya cikin haɗin kai don goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta a hannun gwamnatin Yahudawan sahyoniya ta ƙasar Isra’ila da ke mamaye da ƙasarsu da ƙarfi.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da zanga-zangar a kusan dukkan ƙasashen duniya da suka haɗa da Amurka, Birtaniya, Jamus, Faransa, Australia, Kanada, Ghana, Jamhuriyar Nijar, da kuma Nijeriya a wasu jihohi da dama, ba tare da wata barazana ko hari ba, sai dai sai a Jihar Kaduna (Kaduna da Zariya).

Ya ce, a nan Nijeriya, an kwashe sama da shekaru 37 ana bikin ranar Qudus ta duniya. Shahararren taron shekara ne amma kuma a ranar Juma’a 29 ga Afrilu, 2022, an kai wa zanga-zangar hari a Kaduna da harsashi masu rai da hayaƙi mai sa hawaye, wanda ya yi sanadin kashe wani mutum mai suna Mustafa Abubakar Wagini (mai shekaru 28), wanda kasance ɗalibi ne ajin ƙarshe a jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, da kuma raunata wasu 9. An kama mutane takwas a hanyarsu ta komawa gida kuma yanzu haka suna tsare a hannun ’yan sanda.

Ya ci gaba da cewa, muna kallon abin da ’yan sanda suka yi a Jihar Kaduna a matsayin rashin tunani da rahsin wayewa, wanda kamata ya yi su mayar da hankulansu a kan rashin tsaro da ke addabar ƙasar. Kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (Kamar yadda aka yi wa kwaskwarima) ya tabbatar da ’yancin gudanar da addini kamar yadda sashe na 38(1) da sashe na 40. Mu a nan muna Allah wadai da wannan kisan gilla da ake yi mana.

Haka zalika, wakilin ’yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Zariya, Shaikh Abdulhamid Bello, ya yi watsi da ikirarin rundunar ‘yan sanda na cewa sune suka ƙona masu ofishi a Kasuwar Mata da ke Sabon Gari Zariya a ranar Juma’ar da ta gabata.

Shaikh Abdulhamid Bello, ya musanta zargin da aka yi masu ne a lokacin da ya ke zanatawa da manema labarai.

Shaikh Abdulhamid Bello, wanda ya yi kira ga jami’an tsaro su gaggauta sakin ‘yan’uwansu sama da 70 da jami’an tsaro ke tsare da su tun bayan zanga-zangar ‘Ranar Qudus’ a Zariya, ya yi amfani da wannan damar, inda ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta sakar wa Shugabansu Shaikh Zakzaky da mai ɗakinsa takardunsu na tafiya don su fita ƙasashen waje neman magani.

Ya ce, a ƙarshe muna kira ga duk masu hannu da shuni da su cigaba da kira ga Gwamnati da ta daina waɗannan hare-hare, sannan kuma gwamnati ta saki fasfo ɗin Jagoranmu Sheikh Ibraheem Ya’qoub El-Zakzaky da matarsa ​​Malama Zeenatudeen Ibrahim ba tare da wani sharaɗi ba. Haka kuma, muna kira ga ’yan uwa ’yan Nijeriya da su nemi tsaro, adalci, daidaito da ’yanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *