Daga AMINA XU
Abokaina, yau na zana wani Cartoon dangane da wata ƙasa mai matuƙar cin moriya daga yaƙe-yaƙe. Amurka ta yi kirarin cewa, ba za ta tura sojojinta zuwa Ukraine, amma a wani ɓangare ta rika baiwa Ukraine taimako na soja, matakin da ya zuga wuta a yankin. Kakakin fadar White House ta Amurka Jen Psaki ta bayyana cewa, taimakon soja da Amurka ta baiwa Ukraine ya kai dala biliyan 1.7, tun bayan da Rasha ta ɗauki matakin soja na musamman.
Ko Amurka za ta yi abin da ba za ta ci moriya ba? Amsa ita ce a’a. Franklin Spinney, wanda ya taba aiki a matsayin mai ba da shawara a ofishin ministan tsaron ƙasar Amurka na tsawon shekaru 26, ya kuma taɓa bayyana cewa, masana’antun samar da makamai na ƙasar za su zuga wuta ga tarzoma tsakanin Rasha da Ukraine.
Don sa al’umma su ji tsoron Rasha, da nufin neman damar ƙara kasafin kudin makamai, kuma za su ci moriya a dogon lokaci bisa tarzoma dake ƙara tsananta a tsakanin Rasha da Ukraine da dai sauran yankuna.
(Mai zane: Amina Xu)
