Xi ya ƙarfafa gwiwar matasa da su taimaka wajen inganta dogaro da kai kan fasahar sararin samaniyar ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ƙarfafawa matasa da ke aikin sararin samaniya gwiwa, da su ƙara ba da gudummawa, wajen ganin ƙasar Sin ta ƙara dogaro da kai a fannin kimiyya da fasahar sararin samaniya.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin ƙoli na JKS, kana shugaban kwamitin ƙoli na soja, ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin da yake amsa wasiƙar da tawagar matasan da ke aikin gina tashar binciken sararin samaniya a rukunin kimiyya da fasahar binciken sararin samaniya na ƙasar Sin suka rubuta masa.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa