Mutane 122 da ƙungiyoyi 33 sun karvi lambar yabo ta bikin ranar matasan ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

A yau Talata, ƙasar Sin ta fidda jerin sunayen mutanen da suka samu lambobin yabo na ranar 4 ga watan Mayu, wato bikin ranar matasan ƙasar Sin, an ba da lambobin yabon mafi daraja ne ga matasan Sinawa gabanin gudanar da bikin ranar matasan sakamakon irin gudunmawar da suka baiwa ƙasa.

Jimillar ɗaiɗaikun mutane 122 da ƙungiyoyi 33 ne suka samu nasarar shiga jerin sunayen. Kuma an zabo su ne daga ɓangarorin kiwon lafiya, da injiniya, da sashen kashe gobara, da matuƙin jirgin sama, da masu binciken kimiyya, har zuwa malaman makarantu, da ɗalibai, da fagen wasanni, da jami’an ƙananan hukumomi, da manoma, da masu aikin jigilar kayayyaki.

Mai fassarawa: Ahmad