Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga taron ministocin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS

Spread the love

Daga CMG HAUSA

A yau Alhamis ne shugaban ƙasar Sin Xi jinping, ya gabatar da jawabi a yayin buɗe taron ministocin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS ta kafar bidiyo.

Cikin jawabin na sa, Xi Jinping ya ce a halin yanzu, dalilan dake haifar da rashin kwanciyar hankali, da rashin tabbas, da rashin tsaro a harkokin ƙasa da ƙasa na ƙara bayyana. Amma duk da haka, jigon wannan zamanin da muke ciki na zaman lafiya, da neman ci gaba bai canza ba, kaza lika burin al’ummun duniya na samun kyakkyawar rayuwa bai sauya ba, haka kuma, fatan sassan ƙasa da ƙasa na aiki tare kafaɗa da kafaɗa, da haɗin gwiwa domin cimma moriyar juna shi ma bai canza ba.

Bugu da ƙari, Xi ya jaddada cewa, tarihi da ainihin abubuwan da ke faruwa na nuna cewa, yunƙurin wata ƙasa guda na samar da tsaron ƙashin kan ta, yayin da wata ke fuskantar barazana, ba abun da zai haifar sai ruɗani. Don haka a cewar sa “Domin bunƙasa zaman lafiya da tsaron duniya, a baya bayan nan, na gabatar da shawarar samar da tsaro ta ƙasa da ƙasa”.

Shugaban na Sin ya ce, ya kamata ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS su karfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin gwiwar tsaro, su kuma ci gaba da tattaunawa, da tsara ayyuka tare, don gudanar da batutuwan ƙasa da ƙasa da na shiyyoyi yadda ya kamata. Kaza lika ya dace su marawa juna baya, wajen kare muhimman moriyar kawunan su, su martaba ikon mulkin kai, da tsaro da moriyar ci gaban juna.

Kaza lika su nuna rashin amincewa da danniya da siyasar nuna fin ƙarfi, su kuma yi adawa da cacar baka, da ɗaukar matakan yin fito na fito da juna, tare da gina al’ummar duniya mai cikakken tsaro.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, ci gaba buri ne na dukkanin ƙasashe masu karsashin kasuwanni da ƙasashe masu tasowa. Don haka ya kamata ƙasashen nan 5 su tattauna, tare da yin musaya tare da karin ƙasashe masu karsashin kasuwanni da ƙasashe masu tasowa, a fannin inganta fahimtar juna da amincewa juna, su ƙarfafa haɗin gwiwa, da fadada moriyar hadin gwiwa, su ingiza matakan ci gaba, tare da ba da ƙarin gudunmawar cimma nasarar kyakkyawan fata, na gina al’umma mai makomar bai ɗaya ga dukkanin bil adama.

Mai Fassara: Saminu

By Editor