Daga CMG HAUSA
Ofishin kandagarki da hana yaɗuwar COVID-19 na birnin Shanghai, ya faɗa a ranar Litinin cewa, daga ranar 1 ga wwatan Yuni, birnin zai buɗe hanyoyin shiga unguwannin jama’a, da ayyukan sufurin jama’a da zirga-zirgar ababen hawa, a yayin da birnin ke murmurewa daga ɓarkewar COVID-19 da ta fara a watan Maris.
Bugu da ƙari, birnin ya ƙaddamar da matakan tallafawa tattalin arziki a ranar Lahadi, ciki har da rage wasu haraji kan motocin da za a saya.
Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya
