Buhari ya gana da gwamnonin APC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin APC a Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Talata a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya halarci taron wanda ya gudana na tsawon sa’o’i huɗu.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ba a san takamammen abin da Shugaba Buhari ya tattauna da gwmanonin ba.

Hatta Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da ya kasance shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, shi ma ya ki cewa komai game da sakamakon taron.

Sai dai, NAN ya kalato cewa taron nasu na da nasaba da batun Babban Taron jam’iyyar wanda zai gudana daga 6 zuwa 8 ga Yunin 2022.