Daga AMINA XU
Abokai, yau na zana wani Cartoon dangane da harbe-harben bindiga da suka yi ta faruwa a ƙasar Amurka, kuma da hakan ina nuna alhini ga yaran da suka rasu sakamakon harbe harben bindiga da suku rutsa da su a Amurka, musamman ma yara 19 da suka rasa rayukansu kwanan baya a jihar Texas na ƙasar.
‘Yancin mallakar makamai na samar da sauki ga masu aikata laifuka a ƙasar, matsalar da ta addabi yaran ƙasar sosai. Bai kamata irin wannan matsala ta bullo a cikin wata ƙasa dake iƙirarin kare hakkin Bil Adama da martaba dimokuraɗiyya ba.
Dole ne ‘yan siyasa da masu jarin hujja su farka, kada su jefa yara a cikin tsoro, da nuna rashin kulawa da su. Da fatan waɗannan yaran da suka rasu za su huta cikin kwanciyar hankali a aljannar da babu fitar harsasai a cikin ta.
Mai zana: MINA
