Daga HASHIM ABDALLAH
Daga masu son shigarta, har zuwa kan masu rarraunar fahimta gare ta da masu neman fahimtar mece ce ko kuma dalilan adafin sunanta da sha’uku-sha’uku, duk ku buɗe kunnuwanku.
Ma’anar 13×13 Thirteen-Thirteen ko in da Hausa ne, wato sha’uku-sha’uku.
Ƙungiya ce samarwar mutane 13. Haƙiƙa kuma alkhairi ne, kamar yadda taken tafiyar yake, da aka yi imani zai ‘yanta ‘yan Najeriya domin samar da rayuwa mai inganci ko inganta rayuwar ta fuskoki daban-daban gaba da siyasa ko waƙar siyasa ko kamfe. Ba ta da wani maqiyi sai maƙiyin al’umma. A dalilin hadafi na ‘yanta ƙasa, lallai 13×13 ta kafu ne mahadi-ka-ture, wato har illa masha Allahu.
Wato an kafa wannan yunƙuri ne da manufar ɗago da masu fasaha da masu baiwa, daga mawaqa, marubuta jaruman fim, ‘yan wasan kwaikwayo ko ɗago da darajar waɗannan masu fasaha a kowanne fage na basirar da Allah Ya ba su a siyasa ko waƙen al’umma ko wa’azi ko don harshe wato adabi a dunƙule. Yunƙurin da manufar nuna kimarsu ko irin rawar da suke takawa ko zasu takawa fiye da gaban a aikin fasahar ko bayan wannan baiwa, abubuwan da suka haɗa da neman cigaban al’umma kuma domin tallafa wa al’ummar da ciyar da ita gaba, bisa jagorancin manyan mawaƙa da sauran masu fasaha da basira da kafatanin masu ruwa da tsaki a wannan fagage da aka ambato. Tafiyar harkar nau’ukan adabi domin adibai da janibinsa.
Yana da muhimmanci mu fahimci tafiyar ba ta siyasa ba ce, kuma tafiyar ta siyasa ce domin akwai tunanin ceto ƙasar da fafutukar samuwar shugabanni nagari a kowacce jam’iyya kuma bisa yarjejeniya da fafutukar talakawa da yarjewarsu domin ake cika mu su alƙawari da samar da shugabanni nagari, domin wayar da su kan manufofin nusar da su muhimmanci irin nasu, a matsayin gudunmawar mawaƙa.
Wannan ƙungiya tana da shugabanci, kuma shugaba na ƙasa shi ne, Dauda Kahutu Rarara da Kwamitin gudanarwar jihohi na ƙasa ƙarƙashin babban mawaƙi El’mu’az Birniwa. Babban marubucin fina-finai Ibrahim Birniwa ya zama mataimakin shugaban kwamitin siyasa na ƙasa, yayin da shugaban shirye-shirye, kuma mataimakin babban manaja na gidan talabijin na Arewa24 Rabiu Gumel ne shugaba reshen Jihar Jigawa.
Sannan kuma waɗannan jigogi 13 sun haɗa da:
1, Dauda Kahutu Rarara
2, Aminu Ladan Alan Waƙa
3, El’muaz Birniwa
4, Adam A Zango
5, Ali Jita
6, Umar M. Sharif
7, Yakubu Muhammad
8, Daddy Hikima (Abale)
9, Kamilu Koko
10, Baban Cinedu
11, Nura M. Inuwa
12, Aisha Humaira
13, Abubakar Bashir Maishadda

A halin yanzu akwai rassa su ma masu muƙamai 13 a jihohin
Kano, Kaduna, Jigawa, Katsina, Gombe, Kebbi, Niger, Borno, Adamawa, Plateau Nassarawa da sauransu.
Yana da kyau mu ƙara fahimtar cewa, a kowacce jihar akan samu mutane fasihai kuma adibai da jaruman fim a matsayin shugabanni ko mambobi, gami da mawaƙan yabon Annabi (S) inda a Kanon Dabo jigon waƙen Annabi, Malam Bashir Dandago. Abin dai gwanin ban sha’awa.
Wannan yunƙurin da ƙungiya ta 13×13 yana da taken “Alkhairi ce” kuma akwai niyya da nufin karaɗe Najeriya inda ko a kudu an ba da ƙarfin farawa da Fatakwal (Port Harcourt). Yunƙurin na da manufar tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da tallafa wa marayu da gajiyayyu da mutan gidan yari.
Yunƙurin ba ruwansa da jam’iyya sai dai ya duba ɗan takara nagari domin mulkar jama’a.
