Daga LUBABATU LEI
Bullar cutar ƙyandar biri a kwanan nan a wasu kasashen Turai da Amurka ta yi matukar jawo hankalin jama‘a. Sai dai wasu kafofin yaɗa labarai na ƙasashen yamma sun sha yin amfani da hotunan ‘yan Afirka da suka harbu da cutar a lokacin da suke ba da rahoton ɓullar cutar, duk da cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta sha jaddada cewa, akasarin waɗanda suka harbu da cutar a ƙasashen Turai da Amurka ba su taba zuwa Afirka ba.
A game da wannan, ƙungiyar ‘yan jaridar waje a Afirka (FPPA) ta fitar da sanarwa, inda ta bayyana rashin jin daɗinta cewa, hakan zai taimaka ga nuna bambanci ga al’ummar Afirka tare da dora musu laifin cutar. Ta kuma ƙara da cewa, “Ko kafofin na neman kare tsabtar fararen fata ta hanyar shafa wa baƙaƙen fata baƙin fenti.”
Wani mai bibbiyar shafin twitter ma ya ce, “idan ka duba hotunan, za ka yi zaton a Afirka ne cutar ta ɓulla, sabo da yadda kafofin yada labarai na ƙasashen yamma suka nuna hotunan hannayen ‘yan Afirka a rahoton. Amma da ka karanta bayanin, za ka gane cewa, ba shi da nasaba da Afirka.”
Wannan ya sa mu tunawa da yadda kafofin yaɗa labarai na kasashen yamma suka yi ta kokarin siyasantar da cutar Covid-19 a farkon ɓarkewar, don neman shafa wa ƙasar Sin baƙin fenti.
WHO ta sha jaddada cewa, cuta ba ta san ƙasa ba, domin tana iya ɓulla a ko’ina a duniyarmu, tare da haifar da tasiri ga al’ummomi duk ƙabilunsu da launin fatansu da kuma arzikinsu. Idan har ana maganar kwayoyin cuta, babu abin da fararen fata suka fi sauran al’umma da shi. Cuta abokin gaban ‘yan Adam ce, don haka, a duk lokacin da cuta ta bulla, kamata ya yi ‘yan Adam su haɗa kansu, a maimakon neman shafawa wasu bakin fenti.
Mai zane: Mustapha Bulama
