Almundanar biliyan N80: EFCC ta sako Ahmed Idris

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta tabbatar da sako dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris.

Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na hukumar, Mr Wilson Uwujaren ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ranar Alhamis a Abuja.

Jami’in ya ce an ba da belin Idris ne bayan da ya cika dukkan sharuɗɗan belin da aka gidanya masa.

Idan za a iya tunawa, EFCC ta cafke Idris ne ranar 16 ga Mayu bisa zargin yin sama-da-faɗi da Naira biliyan 80 mallakar gwamanti.

Bayanan EFCC sun nuna Idris ya yi amfani da hanyoyi daba-daban waje wawushe kuɗin, ciki har da amfani da ahali da makusantansa.

Hukumar ta ce, ta kama Akanta-Janar ɗin ne bayan da ya gagara amsa gayyatar da ta yi masa a lokuta mabambanta.

By Editor