Idan ana gadon hikimar rubutun littafi to na gada, inji Asma’u Abubakar Jasmine

“Akwai zumunci da soyayya mai ƙarfi a tsakanin marubuta”

“Ina da burin yin rubutun da zai kawo sauyi a ƙasata”

Ba kasafai kake jin labarin ýaýan marubuta sun yi gadon iyayensu a fagen rubutun adabi ba, ko da yake ma ba duk ýaýan malamai ne ke zama masu ilimi ba. Kowa na zuwa duniya ne da irin baiwar da Allah ya halicce shi da ita. Kamar yadda ita ma wannan matashiyar marubuciyar Asma’u Abubakar Musa mai laƙabi da Jasmine take kallon kanta da irin gudunmawar da take bayarwa a harkar rubutun adabin Hausa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, marubuciyar wacce jigo ce a harkokin ƙungiyoyin marubuta da suka haɗa da Manazarta Writers Association da Jos Writers Club ta bayyana irin kyakkyawar alaqar da ke tsakanin marubutan Hausa na ƙungiyoyi daban daban.

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

MANHAJA: Zan so mu fara da jin tarihinki a taƙaice.
JASMINE: Sunana Asma’u Abubakar Musa wacce aka sani da Jasmine. Ni haifaffiyar garin Jos ce, a nan na girma kuma har na yi karatuna, kuma har yanzu ina ci gaba da neman ilimi.

A ina kika samu laƙabin Jasmine?
Laƙabin Jasmine ya samo asalin ne daga makaranta, sunan abokan karatu na suke kirana da shi kenan. Saboda son da nake yi wa furen Jasmine Flower ne ya sa ake kirana da sunan, sai daga baya kuma sai aka cire Flower ɗin ake cewa Jasmine kawai, sai ga shi sunan ya bi ni.

Mene ne ya baki sha’awa da harkar rubuce rubucen adabi?
Tun da na taso gaskiya ina da yawan karance-karance, kusan zan iya cewa hakan ne ya ingiza ni harkar rubutu da kuma baiwar hakan da Allah ya bani.

Yaushe kika fara qirqirar labarin kan ki, kuma da wanne littafin aka fara sanin ki?
Gaskiya ya jima, don a lokacin da na fara rubutu a ɓoye nake yi domin na yi tunanin za a hana ni a gida, saboda qarancin shekaruna a waccan lokacin, sai daga baya kuma da na nuna ra’ayin hakan ban samu matsala ba. Sunan littafin da aka fara sani na da shi shi ne ‘Yaudara’.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa?
Bayan waɗanda na rubuta a waccan lokacin, a yanzu na rubuta guda biyar. Da suka haɗa da ‘Yaudara’, ‘Ɓoyayyen Sirri’, ‘ASP Zarah’, Gayyar Biki’, sai kuma ‘Al’mustapha’..

An ce mahaifiyar ki ita ma marubuciya ce. Wanne littafin ta rubuta?
Haka ne. Mahaifiyata marubuciya ce sosai, a da. Sai dai yanzu ta ajiye rubutun, amma ta rubuta littattafai da dama a ciki akwai ‘Bashin Gaba’, ‘Yusrah’, ‘Kuɗin Gado’ da kuma ‘Koma Baya’.

Za a iya cewa kin gaji basirar rubutu kenan daga wajen ta?
Hikimar rubutu ba abu ba ne da ake gada sai dai ko mutum ya yi koyi da wani da yake yi. Ko da yake masu hikimar magana na cewa, barewa ba ta gudu ɗan ta ya yi rarrafe. Don haka zan iya cewa, idan ana gadon hikimar rubutun littafi na gada nima, sai dai abin da na fi ganin muhimmancin sa shi ne, yadda ta kasance fitilar da ke haska min hanyata a rayuwa.

Waɗanne darussa kika koya daga wajen ta a matsayin ta na marubuciya kuma uwa?
Akwai manyan darussa da na koya a gurinta ta fannin tarbiyya da kuma rubutun da nake yi. A fannin rubutu na koyi abubuwa da dama daga gareta, yadda zan tsara rubutuna sannan na tsarkake alƙalamina, da yadda zan isar da saƙo ta hanya mai sauƙi da al’umma za su amfana da ita.

Wanne saƙo kike ƙoƙarin isar wa a rubuce rubucen ki?
Galibi a duk lokacin da zan yi rubutu ina duba yanayin rayuwar da mu ke ciki ne, sai dai duk da haka na fi mayar da hankali ga jigo uku: soyayya, tsaro da kuma ilimi.

Mene ne burinki nan gaba a harkar rubutun adabi?
Ina da burin wata rana na yi rubutun da zai kawo sauyi a ƙasa ta, musamman ga manyan matsaloli da mu ke fama da su.

Wacce shawara kike da ita ga matasan marubuta ýan uwanki?
Ka da su mayar da hankali wajen tunanin wani abu da za su samu da rubutu, su yi ƙoƙarin wajen ganin cewa sun rubuta abin da zai amfanar da al’umma.

Yaya dangantakar marubutan Hausa na Jos da sauran marubuta na Kano da sassan Nijeriya?
Alhamdulillah, akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninmu. Saboda a tsakanin marubuta gaskiya akwai zumunci mai ƙarfi da soyayyar juna, ba a damuwa daga inda ka fito matuƙar a ka haɗu.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
Akwai karin magana ɗaya da lokuta da dama ta ke tasiri a kaina musamman idan na ji kamar ina son janyewa daga wani abu da na saka a gaba. A Rashin Kira Karen Bebe Ya Ɓata.

Jasmine, na gode.
Nima ina godiya sosai.