Daga LARABI LARABEEN
Lokacin da kiristoci suka kashe ɗimbin mutane a Jos da suka zo wucewa. Kuka ce kad a ɗauki doka a hannu. Shin zuwa yanzu wanne Hukunci gwamnati ta yi wa waɗannan mutanen da suka yi kisan kan?
Lokacin da aka yi wa sojan nan kisan wulaƙanci a Kudu aka yanka su shi da matar da zai aura aka yanke kansu. Aka yanke al’aurar matar aka ɗora a kan cikinta. Aka Haska wa Duniya Saboda wulakanci da tozarci. Kun ji Gwamnati ta ɗauki mataki a kan waɗanda suka yi kisan kan?
Lokacin da Ake Kashe Fulani da dabbobinsu a kudu, kisan wulaƙanci, Wanne mataki Gwamnati ta ɗauka a kansu masu yin kisan?.
To bari na baku wani qaramin Misali da ya faru a kwanakin baya kusan dai shekaru biyu. Da wata yarinya kirista ta ce wani ɗan Arewa direba ya sace ta a Abuja a kan Titin Dutsen Alhaji Kusa da open University. Kiristoci suka yi wa Direban tara-tara ba tare da binciken ƙarya ne ko gaskiya ne ba. Suka saka taya suka Cinna masa wuta. Kun ji Gwamnati ta ce don me ya sa suka ɗauki doka a hannunsu?.
A kudu ba sa jira. Kullum ɗaukar doka suke a hannunsu ko ƙaramin laifi wanda suka raina ya yi musu yanzun nan za su aika da shi lahira. Na sha ganin ana ƙona mutum a Lagos a kan laifin da bai kai ya kawo ba. Bare kuma laifin da la’ananniya Deborah Samuel ta yi. Wanda shi ne ma fi girman laifin da za ka yi wa musulmi ya ji ransa ya sosu, ya kasa jurewa.
Yanzu dai ya isa munafukai ‘yan Arewa izna su gane cewar; ran ɗan kudu kirista ɗaya ya fi ran ‘yan arewa na jihohi 10 da suke kiran kansu da zafafa goma a ranar zaɓe, daraja da muhimmanci.
Domin kuwa an kashe Deborah Samuel a kan vatancin da ta yi wa fiyayyen halitta (SAW). Wanda ko a bible na gaske laifi ne ka zagi kowanne Annabi. Amma hankalinsu ya tashi suna neman a ɗauki fansa. Da namu aka kashe a Kudu, babu abinda zai faru. Cikinmu ne ma ‘yan arewar wasu za su yi rawa da murna su ce ai Allah shi ƙara. Ko don saboda banbancin ra’ayi, ko saboda banbancin aƙida.
A nan soshiyal midiya kuna sane da cewar; ko Gwamna ka zaga a shafinka na Fesbuk ba ma shugaban ƙasa ba, In dai kana Nigeria ko cikin uwarka za ka koma sai an kamoka an hukuntaka? To amma wai an zagi wanda aka halicci Duniya domin sa, muke cin arzikinsa da alfarmarsa. Shi ne har ake samun wasu gurvatattun musulmai a cikinmu suke cewa abinda aka aikata wa wadda ta yi ɓatancin ba dai-dai ba ne. Bayan abinda ta furta ko ga uban mutum ta furta, in dai ka haifu ba ka barin ta haka sai ka ɗauki matakin yi mata dukan tsiya saboda zagi ta yi irin na gatsali da wulaƙanci.
Allah ka ƙara mana soyayyar Manzo Sallallahu Alaihi Wassallam da Iyalan gidansa. Amin summa Amin.
Larabi Larabeen marubuci ne. Ya rubuto daga Kano.
