Daga SAMINU ALHASSAN
Tun bayan fara aiwatar da matakan kullen annobar COVID-19 da ta ɓarke a birnin Shanghai na ƙasar Sin, kimanin watanni 2 da suka gabata, a yanzu haka mahukuntan birnin mai yawan al’umma sama da miliyan 25, sun ce matakan da aka ɗauka sun haifar da “da mai ido”, kuma “kwalliya ta biya kuɗin sabulu”.
Tuni dai aka sanar da tsara sake buɗe birnin, inda ake sa ran daga Alhamis din nan 2 ga watan Yuni, za a buɗe hanyoyin shiga unguwanni, kana za a dawo da ayyukan sufuri da zirga-zirgar ababen hawa, waɗanda dukkanin su matakai ne dake nuna birnin ya farfaɗo daga ɓarkewar wannan annoba.
Bisa shaidu na zahiri, babbar manufar ƙasar Sin ta gaggauta kawar da cutar COVID-19 baki ɗaya da zarar an gano ɓullar ta, ta taimakawa ƙasar matuƙa, wajen dakile bazuwar wannan annoba a sassan ƙasar daban daban. Mun ga yadda wannan dabara ta takaita yaɗuwar annobar a iya wasu birane da yankuna da aka taba samun ɓullarta, aka kuma shawo kan ta cikin nasara.
Muna iya tuna yadda aka aiwatar da wannan tsari a biranen Wuhan, da Zhengzhou, da Fuzhou, da Suzhou, Tianjin, da Shenzhen da Xi’an, yayin da shi ma birnin Beijing ke ƙara ƙaimin shawo kan ɗaiɗaikun alƙaluman bazuwar cutar, musamman ma nau’in Omicron mai saurin yaɗuwa.
Bahaushe kan ce “Mahakurci mawadaci”, ko shakka babu, babban darasin da duniya za ta ita koya daga wannan yanayi shi ne, jurewa matakan killace wuraren da annobar COVID-19 ta yaɗu cikin su, da gudanar da gwaji akai akai, da karɓar rigakafi, karkashin babbar manufar da Sin take amfani da ita, ta gaggauta kawar da cutar a duk inda ta ɓulla baki ɗaya, sune dabaru mafiya dacewa na shawo kan annobar COVID-19 a duniya baki ɗaya, kuma kin bin wadannan matakai, ba abun da yake haifarwa sai asarar rayuka, da gagarumin koma bayan harkokin rayuwa baki ɗaya.
Fassara: Saminu Alhassan
