Zaɓen APC: Amosun da Fayemi sun janye wa Tinubu

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A ci gaba da fafatawa da ake yi tsakanin ‘yan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC don tsayar da ɗan takara ɗaya da zai wakilci jam’iyyar a Babban Zaɓen 2023, an samu wasu daga cikin ‘yan takarar sun janye aniyar takararsu.

Tsohon Gwmanan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun da Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, sun bayyana janyewarsu daga zaɓen fidda gwanin don mara wa tsohon Gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu baya.

Amosun da Fayemi sun bayyan janyewarsu ne a wajen Babban Taron APC da ke gudana a dandalin Eagle Square, Abuja.

Su biyun sun yi kira ga ɗaukacin magoya bayansu a kan su zaɓi Tinubu don cigaban ƙasa.

By Editor