Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya miƙa Tura Jam’iyya ga Asiwaju Bola Tinubu a matsayin wanda zai yi wa Jam’iyyar APC takarar Shugaban Ƙasa a 2023.
Tinubu ya zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC ne bayan da ya lashe zaɓen fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar a Abuja.
Ƙuri’u 1,271 Tinubu ya samu wanda hakan ya ba shi nasara a kan abokan hamayyarsa, irin su tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da ya samu ƙuri’u 316, da kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo wanda ya tashi da ƙuri’u 235 da sauransu.
Sa’ilin da yake jawabin amincewa da nasarar da ya samu, Tinubu ya yi godiya ga Shugaba Buhari da shugabannin APC da gwamnonin APC da daliget na jam’iyyar da takwarorinsa da suka shiga takarar tare haɗe da ɗaukacin waɗanda suka ba da gudunmawarsu wajen cimma nasararsa dangane da nasarar da ya samu.
