Daga BASHIR ISAH
Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya miƙa saƙon taya murna ga Ahmed Bola Tinubu dangane da nasarar da ya samu a zaɓen fitar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC.
Atiku ya aike wa Tinubun da daƙon ne ta shafinsa na Tiwita a ranar Laraba, 8 ga Yunin 2022.
A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar, nasarar da Tinubu ya samu a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyya mai mulki ta nuna cancantarsa.
“Ina yi maka barka Bola Ahmed Tinubu da nasarar da ka samu na zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyarku. Takara ce mai zafi, amma tun da a ƙarshe ka yi nasara, hakan ya nuna cancantarka,” inji Atiku.
Haka shi ma Tinubun, bai rasa taya Atiku murna ba sa’ilin da ya yi nasarar zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP a ranar 29 ga Mayu, 2022.
