Tikitin takarar shugaban ƙasa na APC: Ban taɓa tsammanin zan yi nasara ba – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Zaɓaɓɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce, ya yi matuƙar mamaki saboda bai taɓa tsammanin zai lashe zaɓen fidda gwani ba.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a lokacin da ya ke jawabi bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar Laraba a dandalin Eagle Square da ke Abuja, ya ce, bai taɓa tsammanin samun nasara ba.

“Yau wata rana ce ta tarihi kuma muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya sa muke raye don shaida wannan rana ta yau. Ya wuce jam’iyyar ya zama aikin Nijeriya. Muna matuƙar godiya ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa mai goyon bayansa.

“Ina kuma gode wa Shugaban Majalisar Dattawa. Zan iya jin haushi da kuka yi takara da ni, amma yanzu mun zama ɗaya.

“Ga shugaban jam’iyyarmu, ya bayyana a makonnin baya cewa wasu jaridu da mutane da yawa suna son rubuta tarihin mutuwar wannan jam’iyyar. Amma mun ja daga a matsayin jarumai don kare ta. Abin kunya ga waɗanda tuni suka gina akwatin gawar APC.

“Ga Ƙungiyar Gwamnoni kuwa, haƙiƙa muna cigaba. Muna da yaƙinin cewa wannan al’ummar ta dawo kan turba. Ban san abin da na yi daidai ba wanda ya ba ku kwarin gwiwar tsayar da ni a matsayin ɗan takarar jam’iyya.

“Za mu tsaya domin kawar da masu kutse a cikin jam’iyyar. Babu mai kutse, babu mai ruguzata da zai iya mayar da Nijeriya baya. Dole ne in gode wa mutanenmu da ke sanye da kayan aiki don sadaukarwa da gwagwarmaya don cigaban qasar nan. Za ku sami lada kuma ku ji daɗin guminku.

“Ina jinjina wa matata da ta jure da daɗewa ba na nan, amma na gaya mata cewa na zaɓi siyasa ne a gaba domin ta haka ne hanya mafi kyau da zan iya yin tasiri a taimakon al’umma da sake fasalin ƙasar.”

Yayin da ya ke yabawa sauran masu neman takara da suka fafata da shi, Tinubu ya ce, “gasar ta ƙare kuma waɗanda ba su goyi bayana ba babu abin tsoro. Ba zan zage ku ba. Dole ne mu yi aiki tare don murƙushe PDP da manufofinsu na koma baya.

“Su (PDP) sun bar mu da yunwa, kuma dole ne mu yi duk abin da za mu yi don mu kayar da wakilan talauci, ta’addanci da ƙarya.

By Editor