Shirin tunkarar ambaliya a daminar bana

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Bayanai na baya-bayan nan da ke fitowa daga hukumomin gwamnatin tarayya, sakamakon hasashen da Hukumar Kula da Yanayin Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) ta fitar game da yadda daminar bana za ta kasance, ya tayar da hankalin jama’a da dama a ƙasar nan.

Hasashen da hukumar ta fitar na cewa, za a samu tunzurin teku da rafuka sakamakon mamakon ruwan sama da za sheƙa kamar da bakin ƙwarya, wanda a dalilin haka wasu jihohin ƙasar nan za su fuskanci malalar ambaliya. Jihohin da aka ambata a rahoton sun haɗa da Ribas, Bayelsa, Kuros Ribas, Delta, Edo, Legas, Ogun, da Ondo, waɗanda dukkan su jihohi ne da ke bakin gaɓa, ko kuma suke da igiyar ruwa mai girma da ta ratsa ta cikin su.

Haka kuma akwai wasu jihohi da ke nesa da teku irin su Adamawa, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Binuwai, da Ebonyi waɗanda su ma wannan ambaliya za ta iya yi wa ɓarna. Sauran sun haɗa da Ekiti, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kwara, Nasarawa, Osun, Oyo, Sakkwato, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. Hasashen ya yi nuni da cewa, za a fuskanci tasirin wannan ambaliya kusan a ko’ina a faɗin ƙasar nan.

Abin da wannan rahoto na Hukumar NIHSA ke nunawa shi ne za a samu saukar ruwan sama mai ƙarfin gaske a cikin ƙanƙanin lokaci kuma zai iya ɗaukewa, a dalilin haka rafuka da madatsun ruwa za su iya tumbatsa su haifar da ambaliya. Hakan na iya shafar jihohi 32 da ƙananan hukumomi 233. Wannan hasashe tamkar gargaɗi ne ga al’ummar da ke zaune a wannan yankin, har ma da maƙwaftan jihohi. Sannan rahoton har wa yau yana farkar da gwamnatoci ne don su shirya kuma su ɗauki matakan da suka dace na kiyaye ƙarfin ɓarnar da wannan ambaliya za ta yi, ko ma dai a ceci rayukan al’umma da dukiyoyinsu da za su iya faɗawa cikin wannan iftila’i, idan Allah ya ƙaddara aukuwar sa.

Idan har gwamnatin tarayya ta ɗauki darasi daga bala’in ambaliyar da aka fuskanta a shekarar 2012 wanda ya haifar da asarar rayuka har 363 fiye mutane miliyan 2 suka bar muhallansu, don tsira da rayukan su da rashin muhalli. Babu shakka za a iya kaucewa bala’in da za a iya fuskanta a wannan karon ma, in ba wata rahamar ubangiji ta sauya wannan ƙaddarar ba. A lokacin Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi bayyana cewa, an yi asarar dukiya da amfanin gona da ƙiyasin kuɗin ya fi Naira Triliyan 2.6. Idan za a iya tunawa a lokacin wannan iftila’i ya shafi jihohi 36, kuma an yi hasashen za a kai wasu shekaru 40 nan gaba ba a sake fuskantar irin haka ba.

Tun daga wancan lokacin, an cigaba da samun ambaliya nan da can, saboda dalilai na toshewar hanyar ruwa, fashewar madatsar ruwa, da canjin yanayi,musamman a ƙauyuka da sabbin unguwanni inda ba a fitar da hanyoyin ruwa ba.

Masana ilimin muhalli sun yi ta ƙorafi da bayyana damuwa kan yadda gwamnati ke jan ƙafa game da batun samar da kuɗaɗe a Asusun Kula da Gurɓacewar Muhalli, da aka tanada, domin magance irin waɗannan matsalolin da za su iya tasowa, kamar na yanzu da ake farkar da hukumomi haɗarin da ke tafe. A maimakon haka, kuɗaɗen da ake warewa suna zirarewa ne ta wasu wurare da ake ɓarnatar da su, ba don amfanin al’umma ba. Alhalin ya kamata a ce, an yi wani tanadi da za a yi amfani da shi a duk lokacin da wani mummunan al’amari ya faru ko yake daf da faruwa.

Ya kamata gwamnati da hukumomin da abin ya shafa za su tashi tsaye wajen ganin an samar da wasu matakai na rigakafi, duk da ya ke dai a wasu jihohin damina ta fara sauka, manoma sun fara sharar gona. Shin yaya ake ciki game da batun samar da bishiyoyi da za su zama garkuwa a bakin gaɓar teku ko manyan rafuka, wanda bai yi tasirin da ake so ba? Wacce gudunmawa ya kamata ’yan ƙasa su bayar don kare muhallansu da kewayensu?

Lallai ya kamata gwamnatin tarayya da ta jihohi su himmatu wajen samar da matakan rigakafi, da wayar da kan jama’a ta kafafen watsa labarai da sauran hanyoyi na isar da saƙonni. Da kuma samar da muhallan da za a iya kwashe jama’a a ajiye su na wani lokaci, don kaucewa ɓarnar da ambaliyar za ta iya yi. Sannan har wa yau a samar da magunguna da ruwan sha mai tsafta, saboda kaucewa varkewar annoba da yaɗuwar cututtuka. Gwamnati na buƙatar ƙara mayar da hankali kan tsare-tsaren ta na kare muhalli da yaƙi da gurɓacewar kewayen ɗan Adam, a gwamnatance.

A yayin da duniya ke bukin Ranar Muhalli ta 2022, lallai ne ƙungiyoyin al’umma da hukumomin gwamnati su haɗa hannu wajen yayata gangamin dasa itatuwa, domin yaƙi da kwararar hamada da lalacewar muhalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *