Ƙungiyar matasan APC ta yaba wa Adamu bisa nasarar shirya ingantaccen zaɓen fidda gwani

Spread the love

*Ta yi watsi da barazana gare shi

‘Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Gamayyar Ƙungiyoyin Cigaban Matasa a Nijeriya da ’yan ƙasashen waje (COPY-ND), ta yi watsi da duk wasu zarge-zargen barazana da ake yi wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, kan tsarin da ya dace wanda a ƙarshe ya samar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, cikin kyakkyawar nasara.

A cikin wata sanarwa da babban daraktan ƙungiyar ta COPY-ND, Dakta Aminu Abdullahi Isyaku ya fitar, ya ce, nasarar da kuma sakamakon taron na musamman da aka kammala kwanan nan, wata hujja ce da Sanata Abdullahi Adamu ya yi a kan zargin da ake yi masa na cewa ba ya goyon bayan fitowar HE Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jam’iyyar.

“Sai akasin haka, shugaban ƙasa a matsayinsa na ƙwararre, dole ne a yaba masa bisa yadda ya tafiyar da tarzoma wajen gudanar da zaven fidda gwani na jam’iyya mai mulki irin ta APC da kuma yadda ya ke gudanar da dukkan ayyukansa wanda ya kai ga samun nasarar fitowar mai riƙe da muƙami na jam’iyyar a yau.

“Shugaban jam’iyyar na ƙasa ya nuna iya aiki tare da yin amfani da ƙwarewarsa ta uba a cikin ƙanƙanin lokacin da ya yi mulki domin tafiyar da mabanbantan ra’ayoyi da kuma ra’ayoyin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da ya kai ga zaɓen fidda gwani ba tare da kawo cikas ga fitowar mai riae da tutarmu a babban jam’iyyar ba, HE Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Yana da kyau a san cewa Asiwaju da kansa ya fahimci irin ƙoƙarin da Shugaban ƙasa ya yi a cikin jawabinsa na nasara.”

A yayin da ta ke murnar fitowar Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, sanarwar ta kuma yabawa Sanata Adamu bisa haɗa kan babbar tawagar da kwamitocin tsare-tsare na jam’iyyar suka kafa wadda a yanzu ta haifar da jagaban waɗanda ba su taɓa faɗi zaɓe ba, kuma za su iya kayar da ɗan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar wanda ya saba tsayawa takara kuma ya faɗi zaɓen shugaban ƙasa.

A gare mu a cikin COPY-ND, mun ɗauki hakan a matsayin al’ada a kowace takara ta dimokiraɗiyya don yin shawarwari na cikin gida wanda zai haifar da sulhu a tsakanin dukkanin ‘yan siyasa.

“A matsayinmu na jam’iyya mai mulki, ba za mu iya ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen rikicin tun kafin zaɓen fidda gwani a jam’iyyarmu ba, idan har muna son mu kayar da ɗan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da ya sha kaye cikin sauƙi, kuma wannan tsari ne gaba ɗaya, wanda shugaban na ƙasa muka yi imanin zai iya kaiwa ga nasara.”

Ƙungiyar matasan dai, ta taya Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ɗan takarar jam’iyyar APC da kuma shugaban jam’iyyar na ƙasa murnar nasarar zaɓen fidda gwani.

“Mu na taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shugaban tarayyar Nijeriya mai jiran gado, shugabanmu na ƙasa kuma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari murnar nasarar zaɓen fidda gwani na riƙon ƙwarya, kuma a matsayinmu na ƙungiyar gamayyar ƙasa, mu na kira ga kowa da kowa ya tashi tsaye domin marawa gwamnati baya.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa kuma mai girma shugaban ƙasa ya jagoranci jam’iyyar zuwa ga nasara domin mu samu tarihin mai ɗorewa ga APC a 2023.”

By Editor