Nijeriya 2023: Tsakanin Atiku da Tinubu wa zai zama ango?

Spread the love

•Damar da kowannensu ke da ita
•Ƙalubalen da ke gabansu
•’Yan takarar da za su yi kawo mu su cikas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Manyan jam’iyyun Nijeriya, APC mai mulkin ƙasar da kuma Jam’iyyar PDP babbar mai adawa, sun kammala zaɓukan fitar da gwanayen da za su rufa wa baya, don ganin sun kai ga matakin nasarar ɗarewa kan kujerar shugabancin Nijeriya a zaɓen 2023 mai ƙaratowa.

Jam’iyyar PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, yayin da Jam’iyyar APC ita kuma ta tsayar da tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu waɗanda za su yi karon-batta a zaɓen mai zuwa.

Gabaɗaya ‘yan takarar ba sabbin yankan rake ba ne a farfajiyar siyasar Nijeriya da sanin duk wani tuggu da ƙulumboton da ke cikinta. Kowanne daga cikin ‘yan takarar yana da damarmakin da zai iya amfani da su wajen gwada farin jininsa da karɓuwarsa a wajen al’ummar Nijeriya masu katin zaɓe don kaiwa ga ci.

A hannu guda kuma akwai tarin ƙalubale da kowannen su zai iya cin karu da su kuma su kasance tarnaƙi wajen samun nasararsa.

Kusan za a iya cewa Atiku Abubakar ɗan takarar PDP yana da wasu damarmaki, idan aka yi la’akari da yankin da ya fito kuma yake da mafi rinjayen masu jefa ƙuri’u, wato Arewa, za a iya cewa bai da wata shakka ko barazanar faɗawa rikicin tikiti na Musulmi da Musulmi, wanda ake kallon dole da irin wannan tikitin Tinubu zai iya fitowa, sai dai kuma Atiku ba shi da gwamnati da za ta dafa masa.

Shi kuwa Bola Ahmed Tinubu su ke da gwamnati a hannunsu, yana da aƙalla gwamnoni 20 da Shugaban Ƙasa, Shugaban Majalisar Dattijai, Kakakin Majalisar Wakilai da kuma kafatanin Jam’iyyar APC da ke aljihunsa.

Bola Tinubu yana da tarihin nasara a zaɓe, yana ɗaya daga cikin ire-iren mutanen da Allah Ya ara wa lokaci suke damawa a kowanne fanni na rayuwa. Tinubu bai tava neman wani muqami ba ya rasa, saɓanin Atiku wanda ya shafe shekaru sama da 30 yana neman shugabanci a Nijeriya, amma bai cimma nasara ba.

A taƙaice ma dais hi bai taɓa samun damar hawa muƙami ta hanyar tsaya wa takara da kansa ba. A 1991 ya sha kayin zaɓen gwamnan Jihar Adamawa/Gongola a ƙarƙashin tutar rusasshiyar jam’iyyar SDP, duk da cewa, wasu na ganin cewa, an murɗe masa ne. Haka nan a 1999 bai kai ga an rantsar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Adamawa ba, tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin mataimakinsa. Sauran zaɓukan da Atiku ya tsaya a 2007, 2011 da 2019, duka faɗuwa ya yi.

To, sai dai a fannin ƙwarewa da gogewa a sha’anin mulki da siyasa da diflomasiyya, za a iya cewa ‘yan mazan ya gogu, domin kasancewarsa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa mai faɗa a ji ya dulmiya a duniya lungu da saƙo, domin babban abinda ya ke kuma tabbatar da hakan shine, yadda ya shiga Ƙasar Amurka ya fito gabanin zaɓen 2019, duk da cewa, an ta kurin idan ya je za a kama shi, saboda zargin da ake yi masa a can na tafka almundahanar kuɗi a lokacin da ya ke riƙe da muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa, inda aka yi zargin ya haɗa baki da wani ɗan ƙasar ta Amurka.

Wani abu da ake ganin zai iya kawo wa Tinubu tarnaƙi a takararsa shi ne yadda ake gani a zahiri bai da isasshiyar lafiya da kuzarin da har zai yi ƙarkon riƙe ƙasar, kamar yadda ake waiwayen faruwar irin haka a tsakanin 2003 ga Marigayi Umaru Musa Yar’Adua.

Yadda jama’a da ‘yan adawa kawai suka dinga yi wa Shugaba Buhari cakulkuli game da shekarunsa ya ishi Tinubu izina a zaɓen 2023.

Sauran abubuwan da za su iya taɗiye karɓuwar Tinubu a Arewa shi ne tambarin da yake da shi na ƙin jinin ‘yan Arewa, kamar yadda ake yawo da wata tattaunawa da ya tava yi da wata jarida a birnin Landon cewa, bai yarda da ƙasa ɗaya al’umma ɗaya ba. Wannan kalami na Tinubu ba ƙaramin cikas zai kawo masa ba yayin yaƙin neman zaɓe.

Bayan haka, an yi wa Tinubu shaidar nuna wa ‘yan Arewa tsana a lokacin da ya yi gwamnan Jihar Legas, inda wani rikici ya haddasa kisan Hausawa ‘yan Arewa sama da 500.

Sai dai kuma manyan ‘yan takarar waɗanda dukkansu attajirai ne na gasken-gaske, sun yi kamanceceniya ta fuskoki kamar haka: Atiku Abubakar na da babban yanki, yayin da Bola Tinubu ke da gwamnati.

Sai dai dukkansu akwai ƙalubalen kacancana ƙuri’a musamman idan muka kalli yankin da kowannensu ya fito.

Bari mu ɗauki Atiku Abubakar, wanda a yankinsa na Arewa zai ɗan kacancana ƙuri’u da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Raniu Musa Kwankwaso, musamman kasancewar jihar Kano na da ƙuri’a mai tarin yawa, sai dai ɓangaren Atiku na iya ganin hakan ba zai zame masa ƙalubale ba idan aka yi duba da gwamnonin PDP a jihohin Adamawa, Sakkwato, Taraba, Benuwai da Bauchi, sai kuma sauran jihohin na Arewa da ake hasashen yawanci ‘yar gida za su yi.

Masu nazari kuwa akan lamuran siyasa suna ganin tasirin da Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso za ta yi kusan zai taƙaita ne a Kano kaɗai, saboda haka ba za ta kawo wa Atiku tangarɗa da yawa ba, domin da ma a 2019 babu ƙuri’un Kano a cikin ƙuri’u sama da miliyan 12 da ya samu.

Hakan ya sanya wasu ke ganin cewa, ta yiwu takarar Kwankwaso za ta fi yi wa ɗan takarar APC barna ne, domin a 2019 ƙuri’un Kano na jam’iyyar ne.

To, sai dai kuma a yankin Kudu da jam’iyyar Atiku ta PDP ta ke da ƙarfi, wato Kudu maso Gabas, zai iya samun cikas sakamakon takarar da Peter Obi ke yi a ƙarƙashin tutar Labour Party (LP), wanda shi ma yana da magoya bayansa daidai gwargwado.
Don haka, akwai hasashen jihohin Ibo za su iya kawo masa cikas, nan ma za su kacancana ƙuri’un da Atiku Abubakar.

Yanzu dai duka manyan ‘yan takarar APC da PDP ɗin dukkansu sun murza kambun neman gadon kujerar Muhammadu Buhari, wanda dukkansu sun kafa yara a cikin gwamnatocin ƙasar tun daga 1999 zuwa yau, kuma a wannan lokaci ne kowane ɗa nagari zai so ya mayar da biki ya kyautata wa ubansa a siyasance.

Yanzu dai lokaci kawai zai tabbatar da waye Nijeriyar za ta aura a 2023! Atiku ko Tinubu?

By Editor