Bugun zuciya ya yi ajalin wani daliget a wajen zaɓen fidda gwanin APC a Abuja

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ɗaya daga cikin daliget na jam’iyyar APC, reshen Jihar Jigawa, Isah Baba Buji, ya yanke jiki ya faɗi ya mutu a yayin da yake shirin zuwa dandalin Eagle Square, wurin da za a gudanar da zaɓen fidda gwani na Shugaban Ƙasa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa Buji ya rasu ne a safiyar ranar Talata a ofishin Jihar Jigawa a Abuja a sakamakon zargin ciwon zuciya.

Marigayin dai shi ne mataimakin shugaban Jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Jigawa ta Tsakiya.

Jami’in hulɗa da jama’a na Jam’iyyar APC na Jihar Jigawa, Bashir Kundu ya tabbatarwa da jaridar The Nation faruwar lamarin.

Ya ce: “Eh, ya rasu a safiyar yau. Ya yanke jiki ya faɗi a ofishin Jihar Jigawa da ke Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti, sai kuma ya rasu kafin ya isa asibiti.

“Lokacin da muka isa asibiti an tabbatar da cewa ya rasu. An ce ya mutu ne sakamakon ciwon zuciya.”