Kimanin mutane miliyan 1.5 ne suka samu rigakafin Korona a Jihar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kimanin mutane miliyan aƙalla miliyan ɗaya da rabi ne suka samu rigakafin Korona a Jihar Zamfara.

Manajan shirin na hukumar kula da lafiya ta Jihar Zamfara, Mustafa Aliyu ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da kasida a taron bita na yini ɗaya da hukumar ta shirya wa ‘yan jarida a jihar a ranar Talata.

Ya bayyana cewa, mutane 853,392 ne suka samu allurar farko, mutane 555,509 kuma sun karɓi kashi na biyu, yayin da mutane 107,209 suka samu maganin ƙara kuzari.

Aliyu ya ce da wannan ci gaban, kashi 33 na al’ummar jihar ne kawai suka samu rigakafin.

Ya bayyana cewa ana ƙoƙarin ganin an samu kashi 70 na al’ummar jihar kafin ƙarshen watan Satumba.

“Muna ƙoƙarin tabbatar da cewa kashi 70 na mutanen jihar sun samu rigakafin kafin ƙarshen watan Satumba na wannan shekara,” inji shi.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da damarsu don garzayawa zuwa ga kowace cibiyar rigakafin Korona domin samun allurar kyauta.

A nashi jawabin, babban sakataren zartarwa na hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Zamfara, Dakta Ismail Tukur, ya jaddada cewa, ana ci gaba da gudanar da rigakafin a ɗaukacin ƙananan hukumomi 14 na jihar.

A cewarsa, Zamfara na da cibiyoyin kiwon lafiya sama da 700 a faɗin jihar kuma sama da 600 irin waɗannan cibiyoyi ne suke gudanar da allurar rigakafin duk wata a jihar.

A nashi jawabin, kwamishinan lafiya na jihar Alhaji Aliyu Abubakar wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar, Aliyu Maikiyo Maradun, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Bello Mattawale a yanzu ta yi ayyuka da dama a fannin kiwon lafiya a jihar.

Ya bayyana cewa gwamnan ya sayo tare da raba motoci sama da 10 domin duba cibiyoyin lafiya a jihar.