Ban ce a ƙirƙiro ma’aikatar ɓarayin daji ba – Sheikh Gumi

Daga WAKILINMU

Fitaccen malamin addinin Musulunci na Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya yi ƙarin haske kan shawarar da ya bayar ta buƙatar a samar da ma’aikatar kula da harakokin makiyaya a Nijeriya.

Yayin zantawa da manema labarai a wani bikin nuna al’adun Fulani a Abuja, Shehin Malamin ya ce wasu kafofin yaɗa labarai sun sauya abin da ya faɗa yana mai ƙaryata rahotannin da ke cewa ya ce “ya kamata gwamnati ta ƙirƙiro ma’aikatar ɓarayin daji.”

“Sun mayar da makiyaya a matsayin ‘yan fashin daji,” kamar yadda malamin ya bayyana a wani bidiyo da kafar talabijin ta Channels ta wallafa a Tiwita.

Ya ƙara da cewa kashi 99.9 na makiyaya masu son zaman lafiya ne, yana mai cewa wasu tsiraru ne kawai ke haifar da wannan tashin hankalin da ake fama da shi.

Tun da farko Sheikh Gumi ya ce ya kamata gwamnati ta ƙirƙiro ma’aikatar kula da makiyaya kamar yadda ta samar da ma’aikatar kula da harakokin yankin Neja Delta.

Ya ce akwai buƙatar a tattauna da su kuma a yi masu wa’azi da wayar masu da kai, “Musulmin ƙwarai ba zai kashe ko raunata wani ba a Nijeriya.”

Ya ce wasu Fulani makiyaya sun bi tunaninsu na cewa “an manta da su a yayin da duniya ke ci gaba.”