EFCC ta kama mutane 19 da ake zargi da damfara ta intanet a Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Hukum Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa EFCC, shiyyar Ilorin ta kama wasu mutane 19 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wani samame da ta kai a Lokoja, jihar Kogi.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin hukumar Wilson Uwujaren, kuma aka raba wa manema labarai a ranar Litinin a Ilorin.

Ya ce jami’an hukumar EFCC masu sa ido ne suka fito da waɗanda ake zargin daga maɓoyarsu a ƙarshen mako, biyo bayan samun sahihin bayanan sirrin da suka yi na damfara.

Mista Uwujaren ya ce waɗanda ake zargin sun haɗa da wani ma’aikacin Corps a jihar, Adamu Shu’aibu, da wasu 18.

“Sauran waɗanda ake zargin sun haɗa da Achimugu Nelson Ojonoka, Victor Atsumbe, Akoh Grace Samuel, Usman Abubakar Sadiq, Jacob Emmanuel, Solomon John, Christian Oyakhilome, Adesanya Adeolu Tosin, Uloko George Ojonugwa da Timothy Eleojo Moses.

“Sauran su ne Negedu Joseph Onuchei, Usman Tenimu, Lukman Musa, Samuel Atadoga, Daniel Atekojo James, Abdulrazaq Iko-ojo Ahnod, Olarewaju John Olumide da Ademola Adegoke Daniel,” inji shi.

Kakakin ya ce bayan kama su, an ƙwato wata mota ƙirar Lexus, maƙudan kuɗaɗe da ake zargi da aikata laifukan da ba su dace ba, da wayoyin hannu daban-daban, Laptop da sauran kayayyakin daga hannun waɗanda ake zargin.

Sai dai ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.