Ƙarancin dakon man fetur ne ya haifar da wahalarsa a ƙasa – IPMAN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta ɗora alhakin ƙarancin dakon man fetur da ake samu daga defo na Legas a dalilin da ya haifar da wahalar man da ake fuskanta a Abuja da sauran sassan ƙasar.

Shugaban ƙungiyar ta IPMAN, Chinedu Okoronkwo ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ranar Litinin a Legas.

Okoronkwo ya yi magana kan yadda layukan mai ke sake dawowa a wasu sassan ƙasar nan, musamman a Abuja.

Ya ce yaƙin Rasha da Ukraine ya kawo cikas ga yadda ake rarraba man fetur cikin sauki.

A cewarsa, a yanzu haka dillalan man da ‘yan dakonsa na fuskantar wahalar ɗauko man daga defo zuwa wasu sassan ƙasar nan.

Ya ce: “Kuɗin da ake kashewa wajen sayen man dizel ya yi matuƙar tashi, inda hakan ya ke janyo wa muna samun faɗuwa.

“A halin yanzu ba zai yiwu a cigaba da sayar da mai kan farashin famfo na Naira 165 ba indai ba a sake duba a kan farashin ba.

“Muna kira ga gwamnati da ta duba halin da ake ciki ta hanyar yin nazari kan farashin kayan ko kuma kawo mana tallafi ga dukkan dillalai domin kawo daidaito a harkar,” inji shi.

Okoronkwo ya yaba wa gwamnati kan yadda ta biya ‘yan kasuwa kuɗaɗen dako kawo yanzu, inda ya ƙara da cewa ya kamata a yi ƙoƙarin biyan basukan da su ke bi gaba ɗaya.