Rahoton ƙarya da Adrian Zenz ya watsa ya tona asirin Amurka

Daga CMG HAUSA

Wata doka mai suna wai hana tilastawa ‘yan Uygur aiki ta Amurka za ta fara aiki nan bada jimawa ba. Kwanan nan, Adrian Zenz, wanda ya sha kitsa ƙarairayi ya sake fitar da wani rahoton dake nuna cewa, wai ƙasar Sin na ƙara tilasta wa mutane aiki. Irin wannan doka tana cike da ƙarairayi, wadda ta tona asirin kasar Amurka, na kawar da Xinjiang daga cikin yankuna masu samar da kayayyaki ga duniya.

Haƙiƙa, kafofin watsa labarai sun ruwaito maganganun tsoffin ‘yan diflomasiyyar Amurka a ƙasar Sin dake cewa, babu wata matsala a Xinjiang, dukkanmu mun sani, amma yin amfani da jihar Xinjiang don rura wutar rikici kan batutuwan da suka shafi tilasta yin aiki, da kisan ƙare-dangi, da kuma keta haƙƙin dan Adam, dabara ce ta tsunduma gwamnatin ƙasar Sin cikin mummunan mawuyacin hali.

Rahoton ƙarya da Adrian Zenz ya fitar a wannan karo, yana cewa, wai duk da cewa shaidun da za’a iya amfani ba su da yawa, amma sabon ci gaban da ake samu, ya sa ake ƙara tilasta wa mutane aiki, har zuwa wasu sana’o’in fasahohin zamani. Amma rahoton bai fayyace wane sabon ci gaba ba ne, kana bai bayyana shaidu da wasu alƙaluma ba, illa karya ce zalla kawai.

A ƙarshen bara, gwamnatin Amurka ta sa hannu kan wani shirin doka mai suna wai “hana tilastawa ‘yan Uygur aiki”, wanda za’a fara amfani da ita tun daga ranar 21 ga watan Yunin bana. Dokar za ta hana Amurka shigo da hajojin Xinjiang. Wato ta hanyar fakewa da batun haƙƙin dan Adam, wannan doka za ta hana ci gaban Xinjiang, da kwace damar samun bunƙasuwa na mazauna yankin, kuma wannan take keta haƙƙin dan Adam ne a Xinjiang.

Kusan makwanni biyu da suka wuce, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi jawabi kan manufofin gwamnatin Amurka game da ƙasar Sin, inda ya ambaci wasu muhimman kalmomi uku da suka haɗa da, zuba jari, kulla kawance, da yin takara. Bisa fahimtar Amurka, yin takara shi ne matsa lamba ga abokan takara ta hanyar shafa musu baƙin fenti, da kuma keta ƙa’idojin kasuwancin ƙasa da ƙasa, to, abin da mutum ya shuka, shi zai girba.

Mai fassara: Murtala Zhang