Ƙasar Sin ta nuna adawa da ƙudurin Majalisar Turai kan Xinjiang

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun majalisar dokokin ƙasar Sin ya bayyana adawa da kakkausar murya kan wani sabon ƙuduri da majalisar Turai ta amince da shi, kan halin da ake ciki game da batun kare haƙƙin dan-Adam a jihar Xinjiang.

Kakakin kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama’ar Ƙasar Sin You Wenze ya bayyana cewa, ƙasar Sin tana adawa da magudin siyasa da tsoma baki a harkokin cikin gidan ta da majalisar Turai ke yi, ta hanyar fakewa da batun kare haƙƙin bil-Adama

Manufar yunƙurin da wasu makiya ƙasar Sin dake cikin majalisar dokokin Turai ke yi na neman yin ɓatanci da shafawa manufar ƙasar Sin kan yankin Xinjiang baƙin fenti, ita ce haifar da rashin jituwa tsakanin ƙabilu daban-daban na ƙasar Sin, da neman zubar da kimar ƙasar Sin, tare da daƙile ci gabanta. You ya ƙara da cewa, duk irin waɗannan ayyuka ba za su taba yin nasara ba.

You ya bayyana cewa, batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang, ba batun kare haƙƙin dan-Adam, ƙabilanci ko addini ba ne, amma batun yaƙi da ta’addanci ne da kuma masu neman ɓallewa.

By Editor