Daga CMG HAUSA
A shekaru 10 da suka wuce, kamfanoni da sauran masu dandalin kasuwanci suna ta kara ƙarfin zuba jari a fannin kimiyya da fasaha, lamarin da ya taimaka wajen horas da dimbin ƙwararru.
Alƙaluma sun nuna cewa, yanzu yawan kuɗin da kamfanoni suke zubawa a fannin nazari ya wuce kashi 76 bisa 100 na jimillar kuɗin da zamantakewar al’ummar ƙasar Sin suke zubawa. Kana gwamnatin tsakiyar ƙasar Sin ta fito da manufofi da matakai da dama don ƙarfafa gwiwar kamfanoni da su ƙara zuba kuɗi kan aikin nazari, a ƙoƙarin kyautata ƙwarewarsu ta fannin yin ƙirƙire-ƙirƙire.
Yanzu haka yawan kamfanoni masu fasahar zamani ya kai dubu 330 a shekarar 2021 a duk faɗin ƙasar Sin, a maimakon dubu 49 a yau shekaru goma da suka gabata.
Mai Fassara: Tasallah Yuan
