Daga WAKILINMU
Gwamnatin Tarayya ta bayyana Litinin, 13 ga Yunin 2022 a matsayin ranar hutun gama-gari don Bikin Ranar Dimokuraɗiyya.
Sanarwar haka ta fito ne ta ofishin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola a ranar Alhamis a madadin Gwamnatin Tarayya.
Aregbesola ya taya ‘yan Nijeriya murna game da bikin wannan rana, tare da yin kira ga ‘yan ƙasa da a ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen ganin ta inganta ayyukanta a fannoni daban-daban.
Ya ce, “Yayin da muke bikin Ranar Dimokuraɗiyya, ya kamata mu waiwaya mu dubi ƙoƙarin magabatanmu sannan mu tabbatar da Najeriya ta ci gaba da zama ƙasa dunƙulalliya, mai haɗin kai kuma mai tsaro da zaman lafiya.”
Ya ci gaba da cewa, “Duba da ƙalubalen da muke fuskanta yau a Najeriya, kada hakan ya sa mu rarraba, face mu so juna da gaskiya ta yadda za mu fahimci juna da girmamawa sannan mu zauna tare cikin lumana.”
Kazalika, Aregbesola ya shawarci ‘yan Najeriya da su yi amfani da sabuwar manhajar nan ta tsaro da aka ƙaddamar kwanan nan, wato Nigeria Internal Security and Public Safety Alert System (N-Alert) domin yaƙi da matsalar tsaro da sauransu.
Ya kuma ba da tabbacin Najeriya za ta ci gaba da bunƙasa duba da irin ƙoƙarin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wajen daidaita lamurran ƙasa.
