Daga AMINA YUSUF ALI
Mutumin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, da kuma wanda ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, sun yi asara mai yawa daga duniyoyinsu abinda ya kai jimillar abinda suka rasa, Naira tiriliyon 6.25 ( Dalar Amurka biliyan $14.91).
Al’amarin ya afku ne a ranar Juma’ar makon jiya. Sai dai abin mamakin shi ne, duk da wannan mummunar asarar da suka tafka hakan bai hana su cigaba da riqe matsayinsu na mafi arziki a Duniya da kuma mafi arziki a Afirka ba.
Musk ya tafka asarar ne sakamakon faɗuwa a hannun jarin kamfaninsa na motoci mai suna Tesla wanda ya ragu da kaso -8.66% a kasuwar hannun jari. Wanda wani daga cikin ‘yan kasuwa masu hannun jari a kamfanin ya sayar da hannunsa saboda rashin ganin riba a jarin da ya zuba.
Idan za a iya tunawa, a watan Oktobar shekarar da ta gabata ne dai aka bayyana Musk a matsayin biloniya na farko a Duniya da ya taɓa mallakar abinda ya kai Dalar Amurka biliyan $300 a rayuwarsa. A lokacin mutane suna ta tururuwar sayen hannun jari a kamfanin Tesla. Sai dai kuma jim kaɗan bayan ya cimma wancan arziki ne kuma, sai ci baya ne da kuma asara suke ta samunsa kuma.
A hannu guda shi kuma Ɗangoten, ya yi asarar Naira N4.61 abinda ya kai yanzu ƙarfin dukiyarsa ba zai wuce Dalar Amurka biliyan $14.2 ba. Wanda a shekarar da ta gabata ƙarfin arzikin nasa ya kai Dalar Amurka biliyan $15.
Dukiyar ta Ɗangote ta zama ba ta gaba, ba ta baya ne a sakamakon rashin cigaba a hannun jarin sumuntin Ɗangote. Domin rahotanni sun nuna attajirin yana ta sayar da hannayen jarin kamfaninsa don samun kuɗin da zai kammala ginin matatar mansa da ya sa a gaba. Kamar dai yadda kamfanin bincike na Fitch yayi hasashen cewa wataƙila kanfanin Ɗangoten zai sayar da wasu daga hannayen jarinsa masu yawa a watan Mayun shekarar 2022 domin kammala ginin matatar mansa da ya fara.
