CBN ya umarci bankuna su dinga cazar masu ajiya ladan tura kuɗi ta yanar gizo daga miliyan zuwa sama

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Nijeriya, CBN ya umarci bankunan Nijeriya da su dinga amsar ladan tura kuɗin da suka kai miliyan guda zuwa sama daga masu ajiya. Amma wannan hukunci ga masu asusun ajiya ne na ɗaiɗaikun. Yayin da su kuma asusun haɗaka na kamfanoni, za su dinga biyan kuɗin ne idan an tura kuɗin da ya kai miliyan 10.

CBN ta bayyana haka ne a wata takardar sanarwar da ya wallafa na yin bitar NIBSS a game da hada-hadar kuɗi a yanar gizo.

Hakazalika, bankin na CBN ya ƙayyade adadin iyakacin kuɗin da aka yarda a tura. Wato su ɗaiɗaikun asusun masu ajiya ƙa’idar Naira miliyan 25 su kuma masu asusun haɗaka na kamfani ƙa’idarsu shi ne Naira miliyan 250 ne.

Wannan kuɗin a cewar bankin ana biyan sa ne saboda abinda ka je, kan zo na asarar ga bankin.