Ƙalubalen da ke tattare da yaƙi da talauci a Nijeriya – Rahoton Bankin Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahoton sakamakon binciken da bankin Duniya ya yi, ya bayyana cewa, akwai wasu jerin dalilai da suke kawo cikas ga yaqi da talauci da Nijeriya take ƙoƙarin yi. Waɗannan dalilai sun haɗa da tasirin annobar cutar COVID-19, karayar tattali. Arzikin ƙasa, sanan da dar-dar da ake fama da shi game da yaƙin da yake faruwa tsakanin Rasha da Yukiren su ne abubuwan da suke neman kawo cikas ga yunƙurin kawar da talauci a Nijeriya.

Wasu masana a harkar tatalin arziki a Bankin Duniya, Jonathan Lain da Jakob Engel su ne suka gabatar da wannan rahoto a cikin jawabi da suka wallafa a turakarsu ta yanar gizo. Taken jawabin shi ne, ‘katanga a kasuwanci (zai iya jawo), katanga ga yaƙi da talauci?’ ‘Yadda Nijeriya za ta rungumi kasuwanci don tsamo mutane daga talauci’. Sa’annan a dai wannan wallafa sun ba da shawarar cewa, Nijeriya za ta iya ƙara bunƙasa kasuwanci don sauƙaƙa talauci a ƙasar.

Har’ila yau, rahoton dai ya bayyana cewa, da wuya burin Nijeriya ya cika na cewa za ta fitar da al’ummarta da yawa daga talauci kafin shekarar 2030 domin akwai ƙalubalen sosai a tattare da shi.

Hakazalika, a cewar su da ma ko gabanin ɓullar annobar COVID-19, huɗu daga cikin mutum goma a Nijeriya yana fama da ƙangin talauci. Wato a ƙiyasce mutane miliyan 80 da ma matalauta ne a Nijeriya.

Hakazalika, Annobar COVID-1 ɗin ma da karayar tattalin arzikin ƙasa, da zaman fargaban yaƙin Rasha da Yukiren, har ma da ƙaruwar haihuwa a koyaushe su suka taimaka sosai wajen kawo babban cikas ga lamarin.

Kodayake, masanan sun bayyana kasuwanci a matsayin babbar hanyar warware matsalar talaucin ta hanyar zuba jari a ɓangarori da dama har da sashen fasaha, da yin gogayya da manyan kasuwancin Duniya da haka kasuwancin zai bunƙasa. Hakan zai samar da ayyukan yi, zai ƙara darajar kayanmu na gida, sannan zai rage farashin kayan masarufi dukkansu waɗannan za su taimaka wajen rage zafin talauci da yawan matalauta.

Amma fa a cewarsu, haka ba zai samu ba sai da goyon baya cikakke daga gwamnati. Wato gwamnati za ta iya ba da tallafi ga iyalai marasa galihu da sauran abubuwa. Don haka, a cewar masanan in dai Nijeriya ta ɗauki ɓangaren bunƙasa kasuwanci ba abinda zai hana ta kai wa gaci wajen yaƙar talauci a ƙasar.