Sarkin Kwatarkwashi Alhaji Ahmad Umar, Basarake mafi daɗewa a Zamfara ya rasu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sarkin gargajiya mafi daɗewa a Jihar Zamfara, Sarkin Kwatarkwashi, Alhaji Ahmad Umar, ya rasu Alhamis da ta gabata.

A cewar sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Balarabe Danisa, ga manema labarai cewa, sarkin ya rasu ne bayan gajeriwar jinya yana da shekaru 93 a duniya.

Marigayi Alhaji Ahmad Umar ya kasance basaraken gargajiya mafi daɗewa kuma babba akan karagar mulki ba a Zamfara kaɗai ba, har ma a faɗin Nijeriya bakiɗaya, inda ya kwashe shekaru 61 a matsayin Sarkin Kwatarkwashi.

Sarkin mai shekaru 93, an fara naɗa shi hakimin ƙauye a Samawa ta hannun babban yayansa, wanda a lokacin hakimin gundumar ne, Alhaji Umar.

Marigayi Sarkin Musulmi Sir Abubakar III ne ya naɗa shi sarautar Sarkin Kwatarkwashi a matsayin sarki na 28 ranar 17 ga Maris, 1961.