2023: INEC ta ba wa Atiku da Tinubu mako guda su fitar da mataimaka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ba dukkan ’yan takarar Shugaban Ƙasa da na Gwamnoni daga jam’iyyu 18 wa’adin mako ɗaya su gabatar ma ta da sunan mataimakansu.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da hakan ranar Alhamis a Abuja, yayin wani taronsa da Kwamishinonin hukumar na Jihohi.

Hakan dai na nufin ɗan takarar PDP (Atiku Abubakar) da na APC (Bola Tinubu) da na NNPP, (Rabi’u Musa Kwankwaso) da sauran ’yan takarar dole su naɗa mataimakansu nan da mako zaya mai zuwa.

A cewar Shugaban na INEC, yayin da za a kammala dukkan zaɓukan fidda gwani ranar Alhamis, za a fara naɗa Mataimakan ’yan takarar ne daga ranar Juma’a mai zuwa kuma a kammala cikin mako ɗaya.

Farfesa Yakubu ya ce, “a cikin mako ɗaya mai kamawa daga Juma’a, 10 ga watan Yunin 2022, ana bukatar dukkan jam’iyyu su gabatar sunan ’yan takararsu a zaɓukan matakin tarayya (Shugaban Ƙasa da ’yan majalisun tarayya), kafin nan da ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni.

“Zavukan matakin jihohi kuwa na Gwamnoni da ’yan majalisun Jihohi, za a ɗora sunayensu ne daga ɗaya zuwa 15 ga watan Yuli, kamar yadda jadawalinmu da muka fitar na zaɓukan 2023 ya nuna,” inji Farfesa Yakubu.

Shugaban na INEC ya ce, dukkan jam’iyyun za su ɗora sunayen ’yan takarar ne a shafin da hukumar ta tana da (ICNP) a gurbin kowacce mazaɓa.